Me Ke Hana Ka Mai da Hankali ga Yesu?

Yayinda Yesu da almajiransa ke ci gaba da tafiyarsu zuwa Urushalima, suka shiga wani ƙauye inda wata mata mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. ‘Yar uwarta, Maryamu, ta zauna a gaban ƙafafun Ubangiji tana sauraron koyarwarsa. Amma Marta ta shiga hidimar shirye-shiryen liyafar da ya xauke mata hankali.