Yayinda Yesu da almajiransa ke ci gaba da tafiyarsu zuwa Urushalima, suka shiga wani ƙauye inda wata mata mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. ‘Yar uwarta, Maryamu, ta zauna a gaban ƙafafun Ubangiji tana sauraron koyarwarsa. Amma Marta ta shiga hidimar shirye-shiryen liyafar da ya xauke mata hankali.