Yadda Za a Wanke Ƙafafun Wani

A zamanin Yesu, wanke ƙafa al’ada ce saboda duk hanyoyi ƙasa ne, kuma bayi ne suke yin wannan aiki ga manyan mutane. Almajiran ba su ji daɗi ba lokacin da Yesu ya zaɓi ya yi musu hidima ta hanyar wanke ƙafafunsu.