Abu Ɗaya Da Ya Kamata A Damu Da Shi

Yana kama da wani yanayi daga fim na tsoro: Wani mutum tsirara mai ƙarfin da ya fi na ɗan adam yana zaune a kaburbura. Yakan karya sarƙoƙi, ya yi ihu, ya kuma yanke jikinsa. Wannan mutumin aljannu da yawa suka mamaye shi. Amma wata rana ya hango Yesu daga nesa ya gudu zuwa wurinsa.